1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Koffi Annan a Afrika

March 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4k

Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya kammalla ziyara aikin kwanaki 4, da ya kai a ƙasar Madagaskar.

A yayin da ya kiri taron manema labarai, a filin saukar jiragen samar Antananarivo baban birnin kasar, Annan ya bayyana gamsuwa da masayar ra´ayoyi day a yida shugaba Mark Ravalomanana, mussamna a game da tsarin demokaradiya da yancin dan adam.

A ɗaya gefen, ya gana da jami´un adawa, inda su ka cimma matsaya ɗaya, ta komawa tebrin shawarwari da gwamnati, domin magance rikicin siyasa a wannan ƙasa.

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta tura tawaga ta mussaman, domin tallafawa ɓangarori masu gaba da juna,na Madagaskar, su cimma daidaito, ta hanyar shirya zaɓen da a ke sa ran gudanarwa, a farkon shekara ta 2007.

Idan ba a manta ba, tun daga shekara ta 2002, Madagascar ta faɗa rikicin siyasa, tsakanin magoya bayan tsofan shugaban ƙasa Didier ratsiraka, da ya jagoranci tsibirin, a tsawan shekaru 30, da na shugaba mai ci yanzu.

Mutane da dama, sun rasa rayuka a sakamakon wannan rikici.

A ci gaba da rangadin da ya ke a Afrika, Koffi Annan, ya sauka a Jamhuriya Demokaradiyar Kongo.