Ziyara John Negroponte a Lybia | Labarai | DW | 18.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara John Negroponte a Lybia

Mataimakin sakatariyar harakokin wajen Amurika, John Negroponte, ya kammalla ziyara aikin da ya kai a ƙasar Lybia.

Wannan itace ziyara farko, da wani babban jami´in ƙasar Amurika, ya kai a Tripolie, tun shekaru kussan 50 da su ka wuce.

Jami´in ya tantana da jami´an diplomatiar Libia, a game da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Ta la´akari da angizon Shugaba Ƙaddafi a wannnan yanki na Afrika, Amurika ta gayace shi, yayi iya ƙoƙarin sa wajen, shawo kan hukumomin Sudan, su amince da rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia, a yankin Darfur.

John Negroponte, ya yaba rawar da Lybia ke takawa, wajen lallashin ɓangarorin tawayen Sudan, wanda su ka ƙauracewa yarjejeniyar zaman lahia, domin cenza tunani.

A dangane da mu´amila tsakanin Amurika da Lybia, ya kyautta zaton naɗa jikadan Amurika a birninTripolie, ta la´akari da, kyaukyawan ci gaban da aka samu, tsakanin ƙasashen 2.