1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jendayi Franzer a ƙasar Lybia

March 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5S

Sakatariyar harakokin Amurika, mai kulla da nahiyar Afrika, Jendayi Franzer, ta kai ziyara aiki a Libiya, domin tantana rikicin yankin Darfur, tare da hukumomin wannan ƙasa.

Franzer, ta bayyana goyan Amurika, na tallafawa sojojin shiga tsakani, da ƙungiyar tarayya Afrika ta tura a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Wannan kalamomi na nuna cenjin ra´ayin gwamnatin Amurika,wadda a farko ta nuna buƙatar Majalisar Ɗinkin Dunia ta aika dakarun ta, a ƙarshen wa´adin rundunar ƙasashen Afrika, ranar 31 ga watan da mu ke ciki.

Gwamnatin Sudan, da wasu daga shugabanin Afrika, da su ka haɗa da Muhammar Ƙhaddaffi, na Lybia, da Osni Mubarak na Masar sun nuna adawa da wannan mataki.

Jami´ar ta ce ,gwamnatin Amurika tare da hadin gwirar kasashen kungiyar tsaro ta NATO, na tunani a kan irin tallafin da ya cencenta su baiwa rundunar tsaron Afrika don cimma nasara samar da zaman lahia a yankin Darfur.

Wannan sanarwar, ta zo kwanki kaɗan kamin taron hukumar zaman lahia, ta ƙungiyar taraya Afrika, wada zata tsaida magana, akan makomar rundunar da ta aika a yankin Darfur.