Ziyara Jaques Chirac a ƙasar saudui Arabiya | Labarai | DW | 04.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Jaques Chirac a ƙasar saudui Arabiya

Shugaban ƙasar Fransa Jaques Shirac, ya fara ziyara aiki ta kwanaki 3 a ƙasar Saudiyya.

Shugaban na tare, da rakiyar ministoci 4, na gwamnati da shugabanin manyan kampanonin fiye da 10 na ƙasar Fransa.

A tsawan wannan ziyara, tawagogin ƙasashen 2, za su tantana batutuwa da su ka shafi hulɗoɗin saye da sayarwa ta fannoni daban daban, mussamman,Fransa na buƙatar ƙara ƙarfafa hulɗoɗi da Saudi Arabiyya, ta fannin albarkatun man Petur.

Kazalika, magabatan za su masanyar ra´ayoyi, a game da harakokin diplomatia na dunia.

Akwai daga cikin ajendar wannan haɗuwa, batutuwan rikicin makaman nuklear ƙasar Iran, da na yaƙi da ta´adanci, da rikicin siyasar Labanon, da kuma na ƙungiyar Hamas

Wannan itace ziyara aiki ta 4, da shugaban ƙasar France Jaques Chirac ya kai Saudiyya.