1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jan Pronk a Sudan

Yahouza SadissouMay 9, 2006

Majalisar Ɗinkin Dunia ta tura wakili na mussaman a Sudan.

https://p.dw.com/p/Bu0E
Hoto: AP

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya aika wakili na mussamman a ƙasar Sudan, da yaunin samar ciwo kan ɓangarori daban-daban na ƙasar, su yi anfani da yarjejeniyar da su ka rattaba hannu a kai, makaon da ya gabata a birnin Abuja na Tarayya Nigeria.

Jan Pronk da Majalisar Ɗinki Dunia ta ɗora wa wannan yauni, ya sauka yau a birnin Khartum.

A tsawon kawanaki 3, zai ziyarci ɗaya bayan ɗaya, yankunan Darfur ta arewa, da ta kudu, da ke yammacin ƙasar Sudan inda zai tantana da shugabanin ƙungiyoyin tawaye da kuma na ƙabilu daban-daban mazauna wannan yankuna.

A matakin farko, zai gabatar da buƙatar Majalisar Ɗinkin Dunia, na wanzar a zahiri yarjejeniyar da a ka rataba hannu a kai, tsakain yan tawaye da gwamnatin Sudan.

Idan dai ba a manta ba,ranar juma´a da ta wuce ne, ɓangarorin 2, su ka amince da ajje makamman yaƙi bayan wata da watani, na shawarwari.

A mataki na gaba Jan Pronk, zai tantana da ƙungiyoyin tawaye na JEM da na SLM da su ka ƙauracewa yarjejeniyar, da burin samu haɗin kan su, a saban yunƙurin tabbatar da zaman lahia a yankin Darfur.

Duk da yarjenejiyar da aka cimma, har yanzu a na fuskantar tashe tashen hankulla, kamar wanda su ka wakana jiya, a yayin ziyara mataimakin sakataren majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da bada agaji, Jan Egeland.

A ƙarshen rangadin na sa , zai yada zango a birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia,domin halartar taron ƙungiyar gamaya Afrika, a game da rikicin Darfur.

A jiya litinin, ƙasar Amurika ta fido wani daftari, mai ɗauke da buƙatar gwamnatin Georges Bush, na gagauta tura dakarun kwantar da tarzoma na Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.

Tsakanin yau da gobe, a ke sa ran ,sakaratariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ,za ta gabatar da wannan daftari ga komitin sulhu.

Daftarin na Amurika, ya buƙaci gwamnatin Sudan ta amince da karɓar baƙunci tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia, wadda zata duba mattakan aika dakarun shiga tsakani, na ƙasa da ƙasa a yankin Darfur.

Gwamnatin Khartum, ta bayyana aniyar ta, ta aikatawa a zahiri, alkawarin da ta ɗauka a birnin Abuja, a dangane da haka, ta tsaida ranar 15 ga watan da mu ke, ciki domin fara kwance ɗamara ga dakarun ta, na Djandjawid.