Ziyara Jan Prock a Sudan | Labarai | DW | 10.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Jan Prock a Sudan

Wakilin mussaman na Majalisar Ɗinkin Dunia Jan Prock ya kai ziyara aiki a ƙasar Sudan.

Jami´in ya bada shawara kwance ɗamara yaƙin dakarun sa kai, na Djandjawid, tare da haɗin gwiwar tsofuwar ƙungiyar tawayen SLM, da kuma ƙungiyar tarayya Afrika.

A yayin da ya kiri taro manema labarai a birnin Khartum, Jan Prock, yayi kira ga hukumomin Sudan da su ɗauki wannan shawara ta Majlisar Ɗinkin Dunia da mahimmanci.

Sannan su yi iya ƙoƙarin su, ta fannin cika alkawarin da su ka ɗauka, a yarjeniyoyin zaman lahia, da su ka cimma da yan tawaye ranar 5 ga watan mayu a birnin Abuja na taraya Nigeria.

Wannan yarjejeniya, ta tanadi, gwamnati ta kwance ɗamara yan Djanjawid, da ake zargi da aikata fyaɗe da kissan gilla.

Jan Prock, ya ƙara da cewa Majalisar Ɗinkin Dunia, za ta ɓullo da wani saban pasali, na kwancve ɗamara mayaƙan Djandjawid, tare da sa hannun dukkan ɓangarorin da abun ya shafa.

A dangane da batun tura dakarun kwantar da tarzoma a yankin Darfur, jami´in ya ce, Majalisar Ɗinkin Dunia, ba ta aikata hakan ,ba tare da samun izini ba, daga gwamnatin Sudan.

To saidai, har ya zuwa yanzu hukumomin Khartum na ci gabada nuna adawa da batun.