1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Jallal Talabani a France

Shugaban ƙasar Irak Jallal Talabani, ya yi kira ga hukumomin France, su juya baben rikicin Irak, ta hanyar kulla sabin hulɗodi cude ni in cude ka da ƙasar sa.

Jalal Talabani ya yi wannan jawabi, albakkacin ziyara iakin da ya kai birnin Paris, a yau alhamis.

Idan dai ba amanta ba shugaba Jacque Chirac na France na daga sashun shugabanin da su ka nuna mumunar adawa, ga tura sojoji kasar Irak, bayan kiffar da Saddam Hussain.

A ganawar da yayi da shugaba Chirac, Jalal Talabani, ya ce kofofin Iraki buɗe su ke, ga France,muddun ta na bukatar sabinta hulɗoɗi kasuwanci da na diploamatia.

Ziyara Talabani na wakana a daidai lokacin da hare-haren ƙunar bakin wake babu ƙaƙƙabtawa, ke ci gaba da hadasa asarori masu yawa a ƙasar Irak.