1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jacques Chirac a China

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueV

A ziyara aikin kwanaki 4, da ya kai China, shugaban ƙasar France Jaques Chirac, ya gana da takwaran sa, Hu JinTao.

Magabatan 2, sun tantana a game da al´ammura daban-daban da su ka jiɓacin siyasar dunia, hasali ma rikicin makaman nulkear Corea ta Arewa da Iran.

Chirac da Hu Jintao, sun yi kira ga hukumomin Teheran, su mutunta ƙudurin Majalisar Dinkin Dunia, mai lamba 1696,wanda ya haramtawa ƙasar mallakar makamin nuklea.

Sannan,sun bayyana matuƙar damuwa, a game da gwajin makaman , da Corea ta Arewa, ta yi, a farkon watan da mu ke ciki.

A wata sanarwar haɗin gwiwa, Paris da Pekin,sun yi baki ɗaya, a game da batun ɗage, takunkumin makamai da a ka sakawa ƙasar Sin.

Sai kuma ta fannin tattalin arziki, inda tawagogin China da na France, su ka rattaba hannu, a kan yarjejeniyoyi daban-daban na bunƙasa harakokin kasuwanci tsakanin su.