Ziyara Hu Jin Tao a Zambia | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Hu Jin Tao a Zambia

Shugaban ƙasar China, na ci gaba da ziyara aiki a wasu ƙasashen Afrika.

Bayan Kamaru da Sudan, Hu Jintao a halin yanzu, na ƙasar Zambia, inda ya samu kyaukyawan tarbe, cikin tsawraran matakna tsaro.

Saidai duk da haka, ɗaruruwan mutane sun shirya zanga-zangar nuna ƙin jinnin Sin, da su ke zargi da tatse dukiyar Zambia, sannan kampanonin Sin, da ke ƙasar na bautar da ma´aikata, ta hanyar basu alalbashin da bai taka karya ya karya ba.

A jawabin da ya yi, shugaba Hu JinTao, ya yaba hulɗoɗin diplomatia tsakanin ƙasashen 2, mussamman, ta la´akari da cewar, Zambia ce ƙasar yankin kudancin Afrika, ta farko, da ta ƙulla hulɗoɗi da Sin, yau da shekaru 40 da su ka gabata.

Kamar yadda ya yi a matakai na farko, da na 2, na wannan rangadi, Hu JinTao, ya rattaba hannu, akan yarjeniyoyi da dama, na saye da sayarwa, tare da takrawan sa, na Zambia Levy Mwanawasa.

Sannan Sin, ta yafewa Zambia, bashin da ta tambayo ta, ta kuma ambata saka tsabar kuɗi dala milion ɗari 8, ta fannin tono makamashi.

Nan gaba a yau ne, zai tashi zuwa Namibia, kamin ya ziyarci Afrika ta kudu da Mozambique.