1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Hu Jin Tao a Britania

November 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvLo

Shugaban kasar China, Hu Jin Tao, na ci gaba da ziyara aikin kwanaki biyu, a kasar Engla, inda a yau ya gana da Praminista Tony Blair.

A sakamakon wannan ziyara, an rataba hannu a kan kwangiloli daban daban, tsakanin kasashen 2, na milliyoyin dalloli.

Mahimman kampanonin Britania da za su ci moriyar wannan kwangiloli, sun hada da Kampanonin Inshora da na jiragen sama.

Gobe idan Allah ya kai mu Hu Jin Tao, zai isso a an kasar jamus.

Ya gana jiya ,da sauraniyar Engla, inda su ka tantana a kan batutuwa daban daban, da su ka shafi huldodi tsakanin China da Britania.