Ziyara Host Khöler a Mozambique | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Host Khöler a Mozambique

Shugaban ƙasar Jamus Host Khöler, na ci gaba da ziyara aiki a nahiyar Afrika.

A Maputo babban birnin ƙasar Mozambique, Khöler, ya gana da ɓangarorin siyasa daban-daban, masu riƙe da ragamar mulki da yan adawa.

Kazalika, ya sadu da tsofan shugaban ƙasar Afrika ta kudu, Nelson Mandella, da ya dangata da jarumi, ta fannin kauttata rayuwar Afrikawa.

A wannan rangadi ,shugaban ƙasar Jamus, na tare da rakiyar yan kasuwa, da shugabanin kampanonin na nan Jamus.

Zai kuma anfani da wannan dama, domin duba yiwuwar ƙara bunƙasa huldoɗin cinikaya, tsakanin ɓangarorin2.