1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Horst Khöler a Bosnia

Shugaban ƙasar Jamus Horst Khöler, ya kai ziyara aiki a Bosnia, inda ya bayana goyan bayan kasar sa, ga bukatar bosniyawa ta shiga ƙungiyar gamayya turai.

Saidai aganawar da yayi da hukumomin Saraevo, Khöler ya masu hanu ka mai sanda, a game wajibcin gudanar da cenje-cenje ga tsarin mulki, da habbaka tattalin arziki da kuma kare haƙƙoƙin bani adama, wanda su ne ginshiƙin zama memba ƙungiyar gamayya turai.

A ɗaya wajen tawagogin Jamus da na Bosnia, sun tantana a kan mattakan haɓɓaka mu´amila saye da sayarwa tsakanin ƙasashen 2.

Horst Khöler ya kammalla wannan rangadi, tare da ganawa da sojojin Jamus 300, wanda ke gudanar da ayyukan tsaro a Bosnia, a cikin ƙungiyar dakarun turai ta EUFOR.