Ziyara Havier Solana a Iran | Labarai | DW | 06.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Havier Solana a Iran

Sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana, ya gana yau da Ali Larjani, shugaban tawagar ƙasar Iran, a game da rikicin makaman nukleya.

Solana, ya gabatar wa hukumomin Teheran sabin shawarwarin warware wannan taƙƙadama, wanda su ka samu tabaraki, daga ƙasashe 5, masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, da kuma Jamus.

Ali Larjani, ya bayana wa manema labarai cewar, akwai ci gaba cikin sabin shawarwarin.

A game da haka, Iran zata nazarin su, ta kuma bada amsar da ya dace, a lokacin da ya dace.

Wannan saban tayi, da ƙasashen su ka yi wa Iran, na ƙunshe da roman baka, na inganta hulɗoɗi tsakanin Iran da manyan ƙasashen dunia, muddun ta amince, da wasti da shirin ta, na ƙera makaman nuklea.

Saidai, a jajibirin ziyara ta Havier Solana, shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinejdad, ya jaddada yancin ƙasar sa, na mallakar makamashin nuklea