1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Havier Solana a Belgrade

December 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvHp

Sakataran harakokin wajen kungiyar Gamayya turai Havier Solana ya kai ziyara aiki a Belgrade, inda zai tantana batun Kossovo da Montenegro yankuna 2, na tsohuwar Yugoslavia da ke bukatar samun yancin kai, wanda kuma, tun shekara ta 1999 ke karkashin mulkin Majalisar Dinkin Dunia.

Baban burin da Havier Solana ke bukatar cimma, shi ne na samun daidaita Albanawan Kossovo, masu rinjaye, da ke bukatar ballewa,da Sabiya, da kuma hukumomin Belgrade da su ka hau kujera naki.

A daya hannun, Sakataran harakokin wajen Kungiyar Eu, zai tantata da magabatan Montenegro, da su ka yi alkawarin shirya zaben jin ra´ayin jama´a, a watan Aprul mai zuwa, a game da batun ballewa daga Sabiya.