1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Hamid Karzai a Amurika

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuEP

Shugaban ƙasar Afghanistan Hamid karzai, ya kammala ziyara aikin da ya kai Amurika, inda ya tantana da shugaba Georges Bush, a game da batutuwa daban daban , wanda su ka haɗa da yaki da ta´dancui da kuam rawar da Iran ke takawa a kasar Afghanistan.

A taron manema labarai na haɗin gwiwa da su ka kira shugabannin 2, sun bayyana aniyar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin murkushe yan ta´ada, kamart yadda Karzai ya bayyana.

Saidai a game da rawar da Iran ke takawa, a ƙasar Afghanistan, an samu rashin fahinta, rsakanin Bush da karzai.

Amurika ta zargi Iran da kunna rikici a yankin baki ɗaya, ta hanyar samar da makamai ga yan taliban, to saidai a cewar Hamid Karzai, ba haka al´amarin ya ke ba.

A ɗaya wajen, Bush da Karzai, sun bayyana mahimmanci yaƙi da safara miyagun ƙwayoyi, da kuma harakokin cin hanci da karɓar rashawa, wanda su ka zama ruwan dare a ƙasar Afghanistan.