Ziyara Gordon Brown a Amurika | Labarai | DW | 30.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Gordon Brown a Amurika

Praministan Britania Gordon Brown ya kai ziyara farko a Amurika, tun bayan hawan sa akan karagar mulki, ranar 27 ga watan da ya gabata.

Gordon Brown, ya yi ganawar farko da shugaba Georges Bush, inda su ka tanttana batutuwa daban-daban da su ka jiɓanci mu´amila tsakanin ƙasashen 2, da harakokin diplomatia na dunia, mussaman rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan, da kuma ƙiƙi-ƙaƙar da ake fuskanta, a tantannawar da ake, a hukumar cinikayya ta Majalisar Dunia, wato WTO, ko kuma OMC tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da takwarosin su masu fama da talauci.

Nan gaba a yau shugabanin 2, za su masanyar ra´ayoyi, a game da halin da ake ciki a yakin ƙasar Irak.

A kan hanyar sa ta zuwa Amurika, Praminista Brown ya mussanta raɗe-raɗin da ake, na cewar Britania bisa jagoranci sa, zata yi nesa-nesa da Amurika, ta la´akari da yadda Bush ya kai ƙasar ya baro a rikicin Irak.

Danganta tsakanin Amurika da Britania inji Gordon Brown, „takalmin kura ne mutu ka raba“.

Gordon Brown ya yabawa Amurika,a game da ƙoƙarin ta, na yaƙi da ta´danci a dunia.

Zai kammalla wannan ziyara gobe talata, bayan ya gana da sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon a birnin New York.