Ziyara Georges Bush a Korea ta Kudu | Labarai | DW | 17.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Georges Bush a Korea ta Kudu

Shugaba Bush na Amurika Georghes Bush na ci gaba da ziyara aiki a nahiyar Asia.

A yau ya gana da shugaban kasar Korea ta Kudu Roh Moo-Huyn, inda su ka tantana batutuwa daba daban da su ka hada da makamn nuklea a Korea ta Arewa.

A yayin da su ke wannan tantanawa, fiye da mutane 500 su ka shirya zanga zanga, domin nuna adawa da wannan ziyara, da kuma Allah wadai da siyasar Amurika a kasashen dunia.

Kwalayen da su ke dauke da su,na rubuce, da kalamomi ire iren na Allah wadai da yakin Iraki, da kuma bukatar janrewar sojojin Amurika dubu 32, da ke jibge a Korea ta kudu.

A game day akin na Iraki, yan kunar bakin wake na ci gaba da kai hare hare inda a tsukin kwanakin 2 sojojin Amurika 10 su ka rasa rayuka.