Ziyara Georges Bush a Jamus | Labarai | DW | 13.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Georges Bush a Jamus

Nan gaba a yau shugaba Georges Bush na Amurika, zai gana da shugabar gwmanatin Jamus Angeller Merkell, a birnin Stralsund ,da ke arewa maso gabancin Jamus.

Shugabanin 2, za su tantana batutuwa daban-daban, da su ka shafi rikita rikitar, da ke wakana a dunia, hassali ma,rikicin makaman nukleyar kasar Iran , da harbe-harben makamai masu lizzami, da Corea ta Arewa ta yi, a makon da ya gabata.

Kazalika za su masanyar ra´ayoyi a game da halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, da kuma saban yakin da ya barke jiya,, tsakanin Isra´ila da Hezbollah.

Wannan itace ziyara farko da Georges Bush ya kawo Jamus, tun hawan Angeler Merkell a kan karagar mulki watani 8 da su ka gabata.

Jim kadan bayan saukar sa, Georges Bush ya yaba rawar da Jamus ke takawa a nahiyar turai da kuma a fagen siyasar dunia.

Ya jinjina damtse, ga shugabar gwamnati Angeller Merkell, a kan halin danganta, da cude ni incude ka tsakanin Amurika da Jamus.

Saidai, masu adawa da wannan ziyara ta Geoeges Bush sun yi alkawarin shirya zanga zanga, yau a na Jamus domin yin Allah wadai da dabi´o´in Amurika a fagen siyasar dunia.

A ƙarshen ziyara, Georges Bush, zai issa ƙasar Rasha, domin halartar taron shugabanin ƙasashen ƙungiyar G8.