Ziyara Georges Bush a Irak | Labarai | DW | 13.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Georges Bush a Irak

Shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya kai ziyara ba zata, a ƙasar Irak, inda ya gana da Praminista Nouri Al Maliki, da kuma tawagar sojojin Amurika, dake birnin Bagadaza.

Tun bayan shekara ta 2003, da a ka kiffar da Saddam Hussain, wannan shine karo na farko, da Georges Bush ya sa ƙaffa Irak.

Ziyara ta gudana kwana ɗaya rak, bayan da Bush ya kiri taron, na hannun damar sa, inda su ka tantana ,a game da halin da ake ciki a Irakin.

A tsarin farko, Bush zai tantana da Praminsita Nourou al Maliki, ta hanyar Video, a yau talata.

A ɓangaren hare-hare kuma, mutane fiye da 30 su ka rasa rayuka, a sassa daban-daban na ƙasar, a sakamakon bama baman, da ƙungiyar Alqa´ida, ta harba,a matsayin shan fasa, ga mutuwar shugaban ta, na kasar Iraki, Abu Musab Alzarƙawi.

Ƙungiyar ta bayyana Cheick Abu Hamza Al- Muhajer a matsayin saban jagora.