Ziyara G.Bush a yankin Asia | Labarai | DW | 16.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara G.Bush a yankin Asia

A hanyar sa ta zuwa taron na Apec, shugaban ƙasar Amurika, Georges Bush,na ci gabada rangadi a wasu ƙasashe na yankin Asia.

A matakin farko, na wannan ziyarace ziyarce, ya sauka a Singapour, inda nan gaba ayau, zai gabatar da lacca, a jami´ar ƙasar.

Majiya daga makusantan shugaban Amurika, ta nunar da cewa, zai taɓo batutuwan da su ka shafi tattalin arziki, tsakanin Amurika da Singapour, da ma sauran ƙasashen yankin.

Kazalika, Georges Bush, zai bayyana manufofin gwamnatin sa, a game da girka demokardiya, da kuma ƙarffafa yaƙi da al´ammuran ta´adanci.