Ziyara Frank Walter Steinmeir a gabas ta tsakiya. | Labarai | DW | 06.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Frank Walter Steinmeir a gabas ta tsakiya.

Ministan harakokin wajen Jamus Frank –Walter Steinmeier, yayi kira ga Isra´ila da Palestinu su koma tebrin shawawari, da zumar kai ga ƙarshen rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cenyewa a yankin gabas ta tsakiya.

Steinmeir, ya fara tantanawa da ɓangarorin 2, tun a taron Charm El Cheik na ƙasar Masar.

Ya nunar da cewa, duk da kyaukyawan alamun da ake gani, na warware wannan taƙƙadama, har yanzu akwai sauran rina kaba.

Ministan harakokin wajen Jamus, ya yaba taron ƙasashen larabawa a karshen watan maris da ya gabata, inda su ka yi tayin zaman lahia ga Isra´ala.

Steinmeir ya gana da ministan kuɗin Palestinu, inda su ka tantana, a game da takunkumin da EU, ta ƙargamawa gwamnatin wannan ƙasa.

Nan gaba a yau zai gana da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, kamin ya tanttana gobe da Pramanistan Isra´ila Ehud Olmert.