1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara farko ta Shinzo Abbe a Sin da Korea ta Kudu

Gwajin makaman kare dangin, ya zo daidai lokacin da saban Praminsitan ƙasar Japon Shinzo Abbe, ke ziyara aiki a yankin kudu maso gabancin Asia.

Bayan kasar Sin , Abbe ya sauka yau a Koreya ta Kudu, inda ya tantana da hukumomin ƙasashen 2, a game da al´ammura daban-daban ,da su ka haɗa da rikicin makamn nukleryar Korea ta Arewa.

Sannan Praministan Japon ya yi anfani da wannan dama, inda ya bayana bukatar, ta ƙara ƙarffafa mu´amila tsakanin Sin da Japon , da ta fuskanci gurɓacewa a lokacin Yunichiro Koizumi.

Kafofin sadarwa a ƙasashen Sin da Korea ta Kudu, sun bayyana wannan ziyara, a matsayi wani mataki, mai tasiri ga hulɗoɗin cuɗe ni-in cuɗe ka,tsakanin ƙasashen wannan yanki.