Ziyara Ellen Sirleaf Johson a ƙasar Amurika | Labarai | DW | 16.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Ellen Sirleaf Johson a ƙasar Amurika

Shugabar ƙasar Liberia, Ellen Sirleaf Johson, ta fara ziyara aiki ta sati guda, a ƙasar Amurika.

A ranar jiya laraba , ta gabatar da wannan ƙwaƙƙwaran jawabi, a majalisar dattawan Amurika, inda ta sha taɓi, da guɗa, daga yan majalisun Amurika, na adawa da masu riƙe da ragamar mulki.

Tun bayan Nelson Mandella a shekara ta 1994, Ellen Sirleaf John ce, shugabar Afrika ta farko, da ta samu karamcin gabatar da jawabi gaban majalisar Dattawan Amurika.

Wannan gatanci ,na nuni da alaƙar ƙut da ƙut, da haɗa sabuwar shugabar da hukumomin Amrukia.

A jawabin da ta yi, Sirleaf Johson, ta bayana burin da ta ke ɗauki da shi, na farfado da ƙasar Liberia, bayan shekaru 14 na yaƙin bassasa.

Za kiri yan majalisar na Amurika da su bata haƙin kai a wannan saban yunkurin na ceton Liberia.

Bayan ganawa da sassa daban daban na gwammnati, ranar talata mai zuwa, zata tantana da shugaba Georges Bush.

Kazalika, zata gabatar da jawabi ga komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, sannan ta halarci babbar kasuwar hada hadar saye da sayarwa, ta dunia, dake Wall Street ,inda zata buga kuggen kiran shugabanin kampanoni da masana´antu zuwa Liberia.