Ziyara Ehud Olmert a Jordan | Labarai | DW | 15.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Ehud Olmert a Jordan

Praministan Isra´ila Ehud Olmert, ya bayyana aniyar hawa tebrin shawarwari tare da ƙasashen larabawa, a game da rikicin yanki gabas ta tsakiya.

Olmert, yayi wannan bayyani, a sakamakon ganawar da yayi yau ɗin nan, da Sarki Abdallah na Jordan, albarakacin ziyara aikin da ya kai ƙasar.

Ehud Olmert, ya yaba da tayin zaman lahia da shugabanin ƙasashen larabawa su ka yi masa, a lokacin taron da su ka ƙaddamar a Saudia Arabia, a watan maris da ya gabata.

A ɗaya wajen, ya alƙawarta ci gaba da tantanawa, da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da zumar warware rikicin ta hanyar ruwan sanhi, to sadai ya bayyana shakkun cimma wannan mataki, ta la´akari da abunda ya kira, tumƙa da walwala, da ƙungiyar Hamas ke shiryawa.