Ziyara C.Rice a Isra´ila | Labarai | DW | 01.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara C.Rice a Isra´ila

Tashe –tashen hankula a ƙasar Irak, na daga ajendar ziyara sakatariyar harakokin Amurika Condoleesa Rice a yankin gabas ta tsakiya.

Bayan ƙasashen Masar da Saudi Arabia, a yanzu haka Rice na ƙasar Isra´ila, inda take tantanawa da hukumomi a game da halin da ake ciki a rikicin gabas ta tsakiya, mussamman sabuwar shawara Amurika ta shirya wani taron ƙasa da ƙasa, wanda zai maida hankali, wajen lalubo hanyoyin warware wannan rikici.

Gobe idan Allah ya kai, mu Condoleesa Rice zata ziyarci Palestinu, domin tabbatar wa shugaba Mahamud Abbas goyan bayan Amurika, a rikicin da ya ke da ƙungiyar Hamas.

Wannan itace ziyara farko, da Rice da kai yankin gabas ta tsakiya, tun bayan da Hamas ta mamaye zirin Gaza, ranar 15 ga watan juni da ya wuce.