1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice da Jack Starw a ƙasar Irak

April 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3O

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, da takwaran ta, na Britania Jack Starw, sun kai ziyara ba zata, yau a ƙasar Iraki.

Babban burin wannan ziyara, shine matsa ƙaimi ,ga magabatan Irak domin,girka sabuwar gwamnati.

Tun bayan zaɓen yan majalisun dokoki a watan Desember da ya gabata, har ya zuwa yanzu, ƙabilu da ɓangarori daban daban, sun kasa cimma daidaiton girka gwamnmati haɗin gwiwa

Rice da Straw, sun yi ganawar farko, da shugaban ƙasa Jallal Talabani, sannan, nan gaba a yau za su saduwa, da Praminista Ibrahim Aljafari, da sauran shugabanin Al umma na wanna ƙasa.

Ziyara na gudana, jim kaɗan bayan da runduna Amurika, ta bayyana mutuwar 4, daga cikin sojojin ta.

Sannan, mutane 9 sun rasa rayuka, a yayin tashin wata bam ,a birnin Bagadaza.