1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Condoleesa Rice a wasu ƙasashen kudancin turai

Yahouza SadissouApril 25, 2006

Condoleesa Rice ta fara rangadi a yankin kudanci Turai da ƙasar Girka.

https://p.dw.com/p/Bu0U
Hoto: AP

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice ta fara rangadin kwanaki 4, a yankin kudancin turai.

A yau za ziyarci ƙasar Girka, kamin ta tashi da yamma zuwa Turquia.

A mataki na farko na wannan ziyara Condolessa Rice, ta gana da ministar harakoki wajen ƙasar Girka, Dora Bakoyannis, da kuma Praminista Costas Caramanlis.

Tantanawar da su ka yi, ta shafi hulɗoɗin diplomatia tsakanin Amurika da Girka, da halin da ake ciki a wasu ƙasashen dunia, kamar su Iran, Irak da Sudan.

Wannan ziyara na gudana a cikin wani yanayi na tasatsauran matakan tsaro.

Rahotani daga birnin Athenes sun ce, hukumomi su yi tanadin fiye da jami´an yan sanda, dubu 5 domin, tabbatar da tsaro.

Bugu da ƙari jirage masu durra angullu, na ci gaba da shawagi a sararin samaniya.

Saidai duk da haka, ɗaruruwa mutane, sun shirya zanga zangar nuna ƙyamar Condolesa Rice, da manufofin gwamnatin Amurika, bisa gayyatar jam´iyar Communiste, da kuma hukumar kauttata rayuwar jama´ar ƙasa.

Masu zanga zangar,na ɗauke da kwalaye, rubuce da kalamomi masu kira ga Rice,da ta koma gida , ba a da bukatar ganin ta, a ƙasar Girka.

Sun yi Allah wadai, da matakin da Amurika ke buƙatar ɗauka a game da Iran.

Jami´an tsaro, sun tarwatsa su, ta hanyar anfani da barkonan tsohuwa.

A yanzu haka, jami´an tsaron na cikin shirin ko ta kwan a wurare daban-daban na birnin Athene.

Nan bada da jimawa ba, Condoleesa Rice, za ta tashi zuwa ƙasar Turquia.

A ɗaya hannu wanan randagin na Rice a Turquia, ya zo daidai, da lokacin da shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ke ci gaba da tantanawa da hukumomin Ankara.

A wani taron manema labarai, da ya kira, Mahamud Abbas ya bayyana matsanacin hali, na rashin kuɗaɗen aiki da gwamnatin Hamas ke fuskanta, ya kuma bukaci Turquia, ta sa hannu, domin warware wannan matsala.

A dangane da rikicin da ya ɓarke a makon da ya gabata tsakanin Hamas da Fafah, ya tabara cewa, za shi ɗauki matakan da su ka dace, domin shawo kan wannan rikici.

Bayan ƙasar Turquia, nan gaba a yau, a ke sa ran, Mahamud Abbas, zai ci gaba da wannan rangadi, da zai kashi a ƙasashen Nowe, Finlande da France.