Ziyara Condoleesa Rice a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 02.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Condoleesa Rice a gabas ta tsakiya

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ta kai ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya.

A matakin farko na wannan ziyara, zata gana da Sarki Abdallah na Saudiya, inda za su tantana batutuwa daban-daban da su ka jiɓanci halin da ake ciki a yanki.

Musamman za su maida hankali a kan rikicin makaman nuklear ƙasar Iran, da kuma rikicin Isra´ila da Palestinu sannan da tashe tashen hankulla ƙasar Iraki.

A dangane da rikicin nukleyar Iran ,Rice ta sanar manema labarai cewa, jim kadan kamin tashinta daga Amuruika,ta tantana ta wayar talho, da takwarorinta, na ƙasashe masu kujerun didindin, a komitin sulhu na MDD, da kuma na Jamus, a game da sabuwar hanyar da za su bi domin ɓulkowa wannan taƙƙaddama.

Bayan Saudi Arabia, Condolesa Rice zata ziyaraci Masar , sai kuma Isra´ila da Palestinu.