Ziyara Condoleesa Rice a ƙasar Sin | Labarai | DW | 20.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Condoleesa Rice a ƙasar Sin

Sakatariyar hakrakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gabada ziyara aikinda ta kai a nahiyar Asia.

A yau, ta gana da hukumomin ƙasar Sin, inda su ka tanttana batutuwan da su ka jibanci rikicin makaman nukleyar korea ta Arewa.

Condoleesa Rice, ta gayyaci hukumomin Pekin,su tsawatawa Pyong Yang, ta la´akari, da kyakyawar alaƙa da danganta da ke tsakanin su.

A taron maneman labaran da ta kira, tare da takwaran ta na Sin, Li Zhaoxing, Rice ta bayyana haɗarin da ke tattare da mallakar makaman nuklear ga Korea ta Arewa ,a yankin kudu maso gabancin ASia da ma dunia baki ɗaya.

Amurika ta bayyana buƙatar Corea ta Arewa, ta koma tebrin shawarwari, sannan ƙasashen dunia, mussamman Sin, su aiyyanar da ƙudurin MDD , na saka takunkumi ga Pyong-Yang.

A nasa ɓangare, ministan harakokin wajen Sin, ya kira da ayi takatsantsan, wajen ɗaukar matakan kawo ƙarshen rikicin na Corea ta Arewa.