Ziyara Clinton a Afrika | Labarai | DW | 23.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Clinton a Afrika

Tsofan shugaban ƙasar Amurika Bill Clinton, na ci gaba da rangadi a wasu ƙasashen Afrika.

Bayan Afrika ta kudu, Malawi, da Zambia, a yanzu haka, ya na ƙasar Tanzania, inda a yammacin jiya, ya ƙaddamar da wani shiri, na yaƙi da cutar massasarra cizon sabro a birnin Dar es Salam.

Gidauniyar Clinton Fondation, da tsofan shugaban ke jagoranta, ta ce ta yi nasara rattaba hannu a kann yarjeneniyoyi, tare da kampanoni masu sarrapa maganin wannan cuta, wanda su ka amince da zabtare kashi 90 bisa 100, na parashen maganin, domin baiwa kowa damar kare kan sa, daga bila´in wannan annoba.

A ƙasar Tanzania, a ko wace shekara, a ƙalla mutane dubu 100, mussaman mata da ƙananan yara ke mutuwa, sanadiyar kamuwa da cutar Malaria.

A lokacin da ya gana da hukumomin Zambia, Bill Clinton ya alƙawarta kai masu tallafi, ta fannin yaƙi da cutar Sida, wadda ke ci gaba da hadasa ta´adi a ƙasar.