Ziyara Bush a Russia | Labarai | DW | 15.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Bush a Russia

Shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya kai ziyara aiki a ƙasar Russia, inda ya gana da takwaran sa Vladmir Poutine.

A wata liyafar cin abinci da shgugabanin 2 su ka shirya, sun tantana batutuwa daban-daban da su ka haɗa da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran, da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, da kuma karɓar shigar Russia a sahun ƙasashe, membobin ƙungiyar cinikaya ta dunia, wato WTO, kokuma OMC, da za a yi ranar ranar lahadi mai zuwa.

Bayan adawa da ta nuna, a game da wannan batu, a yanzu Amurika, ta ce a shire ta ke, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar Russia a cikin wannan kungiya ta hada-hadar kasuwa.

Kamin ranar lahadin, Russia ce kasa ɗaya tilo, mai ƙarfin tatalin arziki,da ba ta cikin WTO.

A ɗazunan Georges Bush, ya kammala wannan ziyara, ya kuma tashi zuwa Singapour.