Ziyara Brown a Amurka | Labarai | DW | 29.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Brown a Amurka

Prime ministan Britania Gordon Brown,ya jaddada muhimmancin inganta dangan taka t akut da kut tsakanin kasarsa da Amurka,gabannin ziyararsa ta farko a Washinton ,tunda ya haye karagar mulki a watan daya gabata.Mr Brown yace ingantuwar dangantakar,itace mafi mihimmanci a tsakanin kasashen biyu.Wadannan kalamai na premiern Britanian dai sunzo ne bayan da wani Babban jamiin gwamnatinsa yace,Britania bazata sake hadewa a Manufofin Amurka na ketare ba.Nanda saoi kalilan nedai Gordon Brown zai isa birnin Washinton,inda zai gana da shugaba Goerge W Bush a Camp David,kafin ya wuce birnin New York inda zai jawabi a zauren mdd.