1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Angeller Merkel a gabas ta tsakiya

March 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuOh

Kwana ɗaya bayan kammalla taron ƙasahen larabawa a birnin Ryad na Saudi Arabia, shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkell, ta tantana ta wayar talho, da Sarki Abdalah na Saudia Arabia, a game da sakamakon wannan taro da kuma hanyoyin warware rikicin Isra´ila da Palestinu.

Tanttanawar ta wakana a jajibirin da Merkell zata fara rangadi a yankin gabas na tsakiya, inda z ata gana da Sarki Abdallah na Jordan, da Pranimista Ehud Olmert na Isra´ila, da kuma shugaban hukumar Palestniawa Mahamud Abbas.

Kazalika ranar litinin zata yada zango a ƙasar Libanaon, domin ƙara ƙarfin gwiwa ga Praminista Fouad Siniora.