1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Angeller Merkel a ƙasar Ethiopia

Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel na ci gaba da randagi a nahiyar Afrika.

A yau ta gana da Praministan Ethiopia Meles Zenawi, inda ta yi kira ga hukumomin wannan ƙasa, sun ƙara mutunta demokradiya da jam´iyun adawa.

Kazalika, ta yi kira da babbar murya, a game da wajicin samar da yancin faɗin albarkacin bakin yan jarida, a wannan ƙasa, da ta yi ƙaurin suna, ta fannin ƙuntatawa kafofin sadarwa masu zaman kann su.

A wani taron manema labarai na haɗin gwiwa, tare da Meles Zenawi, Merkel ta yi ƙarin haske, a game da batutuwan da su ka tantana a kai.

Nan gaba a yau, shugabar gwamnatin Jamus, zata gabatar da jawabi, gaban komitin zartaswa na ƙungiyar taraya Afrika da ke birnin Adis Ababa.