Ziyara Alpha Omar Konare a Jamhuriya Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Alpha Omar Konare a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

Shugaban hukumar zartzaswa na Ƙungiyar Taraya Afrika Alhpa Umar Konare, ya kammalla ziyara aikin kwanaki 2, da ya kai a Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Konnare, ya gana da ɓangarorin siyasa daban-daban, a shirye shiryen zaɓen shugaɓan ƙasa, da na yan majalisun dokoki,da za ayi, a yan kwanaki masu zuwa.

Bayan tantanawar da yayi da shugaba Lauran kabila, ya yi masanyar ra´ayoyi da madugun yan adawa Etienne Tchissekedy, to saida, bai samu nasara cenza matakin da jam´iyar addawa ta UDPS, ta ɗauka ba, na ƙaurewa zaɓen.

A yayin da ya ke amsa tambayoyi yan jarida, Alfa Umar Konare, ya sannar cewa, ko da UDPS ko ba da ita ba, za a shirya zaɓe, a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, sannan ƙungiyar AU, zata bi diddiƙin zaɓen, ta kuma amince da sakamakon sa, muddun, a gudanar da shi cikin tsabta.

Sannan ƙungiyar tarayya Afrika, zata tura tawagar sojoji a lokacin zaɓen, da kuma bayan sa, domin taimakawa sabin hukomomi, su maido doka da oda, a faɗin ƙasar baki ɗaya da a halin yanzu, ke fama da rikicin tawaye.