Ziyara Abdusalami Abubakar a kasar Liberia | Siyasa | DW | 05.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyara Abdusalami Abubakar a kasar Liberia

Tsofan shugaban kasar Nigeria, da ke shiga tsakanin rikicin Liberia Abdusalami Abubakar ya kai ziyara a wannan kasa

default

Yau ne stofan shugaban kasar Nigeria, bugu da kari wakilin kungiyar ECOWAS, mai shiga tsakani a rikicin Liberia, Abdusalami Abubakar ke kai zayara aiki a Monrovia.

Abdusalami Abubajar zai kai wanan ziyara ayayin da ya rage kwanaki 6 rak ga zaben shugaban kasa da za ayi ranar 11 ga watan da mu ke ciki.

Babban dalilin wannan ziyara shine na tantanawa da bangarorin siyasa daban daban, bayan yan rigingimun da su ka wakana a karshen watan da ya wuce.

A karshen watan na Satumber, an samu baraka tsakanin kotun kolu ta kasar Laberia, da hukumar zabe mai zaman kanta.

Humar zabe ta NEC ta ware yan takara 5 na zaben shugaban kasa, da ta ce basu cencenta.

Bayan da yan takara su ka shigar da kara, kotun koli ta basu gaskiya, da kuma damar sake ajje wata sabuwar takara,matakin da hukumar zabe, mur ta ki amincewa da shi.

Da dama daga masu kulla da harakokin siyasa a kasar Liberia sun bayana cewa, za a dage zaben, a sakamakon wannan kiki kaka tsakanain hukumomin 2.

Abdusalam Abubakar ya issa Libaria don ciwo kan mataslar.

A jimilce yan takara 24 ne da su ka hada da tsifan shahararen dan kwalan kafar nan, Gerore Woya su ka shiga gasar samun kujerar shugabacin kasar Liberia.

Bayan bayyana sakamakon hukuncin na Kotun Koli, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Frances Johson-Morris ya bayana wajibcin dage ranar zaben.

To amma, sanarawar da hukumar ta fido, ranar 30 ga watan Satumber, na nuni da yiwuwar shirya wanan zabe talata mai zuwa.

Majalisar Dinkin Dunia, da Kungiyar taraya Afrika, sun bada cikkaken goyan baya ga wannan zabuka , wanda za su maida Liberia bisa tafarkin demokradiya bayan shekarau 14 na yaklin bassasa day a hadasa mutuwar dubu dari biyu da hamsin, da kuma rugurguza dukan al´ammuran tattalin arzikin kasar.

Haka zalika, kimanin mutane dubu dari 3 da ashirin ne, yan kasar Liberia ke warwatse a kasashe daban daban na yamacin Afrika, tun bayan barkewar wannan yaki.

A shirye shirye zaben, na yan majalisun dokok,i da na shugaban kasa, Taraya Nigeria, ta turo yan gudun hijira Liberia, fiye da dubu 2.

Don tabbatar da gudanar, da zabukan cikin kwanciyar hankali,Komitin sulhu na Majalisar Dunia, ya yanke shawara kara tsawan wa´adin dakarun kwantar da tarzoma su kimanin dubu goma sha biyar a kasar Liberia.

Shugaban kasa mai rikwan kwarya, Gyude Briant, ya alkawarta cewa, za a shirya wannan zabuka cikin adalci, domin itace hanya daya, mai inganci, da za ta fida kasar daga halin rikicin da ta sami kanta ciki.

 • Kwanan wata 05.10.2005
 • Mawallafi Yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZC
 • Kwanan wata 05.10.2005
 • Mawallafi Yahouza sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZC