Zimbabwe ta kira Jakadanta na Jamus gida
December 11, 2007Talla
Jamus ta soki ƙasar Zimbabwe da kakkausan harshe, game da baƙaƙen maganganun da aka kira shugabar Gwamnatin Jamus da su. Hukumomin na Berlin sun ce hakan abune da ka iya lalata dangantakar dake akwai a tsakanin ƙasashen biyu. A jiya ne ministan yaɗa labarai na Zimbabwe, Sikhanyiso Ndlova ya zargi
Shugaba Merkel da cewa shugaba ce mai nu na wariyar launin fata.
Rahotanni sun ce tuni Zimbabwe ta kira jakadanta na Jamus izuwa gida, don nuna adawa da kalaman shugabar Gwamnatin kan ƙasar. A lokacin da take jawabi a taron ƙolin birnin Lisbon tsakanin Nahiyar Afrika da Turai, Merkel ta soki lamirin Zimbabwe da take hakkoki na bil adama. Merkel ta kuma ƙara da cewa matakin abune dake rage ƙimar Nahiyar ta Afrika a idon Duniya.