Zimbabwe ta karyata rahotannin kafofin yada labaranta | Siyasa | DW | 05.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zimbabwe ta karyata rahotannin kafofin yada labaranta

Gwamnatin Zimbawe ta karayata ratannin da ke cewa tana nan tana jera sunayen yan adawa da take shirin haramtawa fita kasashen waje.

Shugaba Robert Mugabe

Shugaba Robert Mugabe

A makon daya gabata ne jamiyar ZANU tayi anfani da rinjayen da take da shi na biyu bisa uku a majalisar dokokin kasar,ta amince da wasu sauye sauye da zasu baiwa gwamnati damar mayarda gonakin da ta kwace daga hannun manoma farar fata mallakar gwamnati,tare kuma da hana zirga zirga zuwa kasashen waje ga wadanda ta kira masu cin amanar kasa.

A jiya lahadi ne wata jarida mai zaman kanta mai suna Standard ta buga wani rahoto da ke cewa gwamnatin kasar ta Zimbabwe tana jera sunayen yan siyasa da masu fafutukar neman yancin jamaa wadanda sabuwar dokar zata shafa.

Inda jaridar ta ruwaito wata majiya ta jamiyar ZANU-PF na fadin cewa,sashen yada labarai na jamiyar karkashin jagorancin tsohon ministan harkokin waje Nathan Shamuyarira,yana nan yana tsara jerin sunayen wadannan mutane.

Ta kara da cewa farko cikin jerin sunayen shine shugaban adawa Morgan Tsvangirai na jamiyar Movement for Democratic Change MDC, da kuma tsohon ministan yada labarai Jonathan Moyo,wanda ya janye daga jamiyar ZANU-PF kuma yanzu haka yake dan majalisa mai zaman kansa.

Sai dai mukaddashin ministan yada labarai na Zimbabwe Chen Chimutengwende,ya karyata wannan zance,inda yace wannan Magana bata da tushe,ya baiyanawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa ba zai yuwu a baiyana sunayen wadanda dokar zata shafa kafin ta fara aiki ba.

Mai Magana da yawun jamiyar adawa ta MDC Paul Themba-Nyathi,ana shi bangare cewa yayi lokaci ne kawai ake jira da dokar zata fara aiki,yace sanin kowa ne cewa an kirkiro da sabuwar dokar ce domin karya lagon yan adawa.

Paul Nyathi ya kara da cewa,amincewa da yan majalisa sukayi da wannan doka ya tabbatarwa da jamaa cewa gwamnatin jamiyar ZANU-PF,gwamnati ce ta kama karya.

Manazarta na ganin cewa gwamnati tana tsoron barin yan adawa fita kasashen yamma ne saboda dangantaka da tayi tsami tsakanin kasashen yamma da kasar ta Zimbabwe sakamakon zargi da sukeyiwa Zimbabwe da lafin take hakkin bil adama.

A halin yanzu Zimbabwe tana fama da matsalar tattalin arziki,inda ta kai ga Zimbabwen a jiya lahadi ta nemi ta roki hukumar bada lamuni ta duniya IMF da kada ta nemi korarta a lokacin wani taro da zata gudanar ranar tara ga wannan wata domin tattauna batun dinbin bashi da ake bin kasar,dake fuskantar matsaloli kamar karancin man fetur da abinci,wadanda yan adawa suka dora alhakinsa akan,rashin iya gudanarwa ta gwamnatin Mugabe da tayi shekaru 25 tana mulkin kasar.

Shi dai shugaba Mugabe dan shekaru 81 da haihuwa ya zargi yan adawa na gida dana ketare dake kokarin ganin sun tumbuke shi daga mulki saboda kwace gonakin turawa yana baiwa baker fatar kasar da laifin yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

 • Kwanan wata 05.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZv
 • Kwanan wata 05.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZv