ZIMBABWE TA KAME SOJOJIN HAYA HAR GUDA 67.. | Siyasa | DW | 12.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ZIMBABWE TA KAME SOJOJIN HAYA HAR GUDA 67..

Rahotanni daga kasar za Zimbabwe sun tabbatar da cewa sojojin hayar guda 67 babu ko ja gwamnatin ta Zimbabwe zata gurfanar dasu ne a gaban kuliya.

Wan nan mataki a cewar ministan cikin gida na kasar,Kembo Mahdi gwamnatin ta Zimbabwe ta dauke shine bisa hujjar zargin sojojin hayar da shirya makarkashiyar kifar da halattacciyar gwamnatin kasar Equatorial Guinea.

Kembo Mahdi yaci gaba da fadawa taron manema labarai cewa akwai kanshin gaskiya bisa kann wan nan zargi da akewa sojojin hanyar,bisa hakan ya zama wajibi ga kasar ta Zimbabwe karkashin kungiyyar tarayyar Kasashen Africa da kuma mdd ta dauki mataki don kare kifar da halattacciyar gwamnatin da mutanen kasa suka zaba.

Ministan ya daiyi wadan nan kalaman ne jin kadan bayan shugaba Robert Mugabe ya gana da wata tawaga daga kasar ta Equatorial Guinea,dangane da yadda zaayi da wadan nan kamammun sojojin hayar su guda 67.

Wadan nan sojojin hayar dai a cewar ministan cikin gidan na Zimbabwe an kame sune a filin saukar jiragen sama na Birnin Harare a ranar lahadin data gabata tare da wasu mutane uku da suka zo taryar su.

Jirgin saman dai a cewar minista Kembo ya taso ne daga kasar Africa ta kudu tare da sojojin hayar 67 a cikin sa a kann hanyar sa ta zuwa kasar ta Equatorial Guinea.

Wadan nan sojojin haya a cewar gwamnatin ta Zimbabwe sun shirya saduwa ne da wasu yan uwan su su goma sha biyar da tuni aka riga aka tsare a can kasar ta Equatortial Guinea don gudanar da wan nan mummunan aiki.

A waje daya kuma a cewar Minista Kembo Mahdi da zarar jamian yan sandan kasar sun kammala dukkannin binciken daya dace tare da hada bayanai za,a gurfanar da sojojin hayar a gaban kuliya domin tuhumar asu da laifin kifar da halattacciyar gwamnati.

Bugu da kari gwamnatin ta Zimbabwe ta dai zargi gwamnatin Amurka da hannu dumu dumu a cikin wan nan kinibibi da ake shiryawa kasar ta Equatorial Guinea,domin kuwa a cewar Kembo Mahdi daya daga cikin sojojin hayar mai suna Simon Mann ne ya tabbatar da cewa suna da goyon bayan kasar ta Amurka da Biritaniya da kuma Spain.

Ministan cikin gidan na Zimbabwe yaci gaba da fadin cewa Simon Mann ya tabbatar da cewa sun samu taimakon hukumomin leken asiri ne na Biritaniya da kuma Amurka a hannu daya kuma dana Spain dangane da gudanar da wan nan danya danyan aikin.

A daya barin kuma gwamnatin kasar Amurka ta musanta zargin da kasar Zimbabwe da tayi mata na cewa tana da hannu a cikin wan nan makarkashiyar da ake shiryawa ta kifar da gwamnatin kasar ta Equatorial Guinea.

Ata bakin sakataren harkokin wajen Amuerkan Colin Powell,Gwamnatin ta Amurka bata da wata alaka da sojojin hayar da aka kame balle kuma jirgin saman daya kwaso su,a don haka zuki ta mallau ce kawai ake yi mata dangane da wan nan abu daya faru.

Haka itama gwamnatin kasar Spain ta musanta wan nan zargi da cewa abune da bashi da tushe balle kuma makama.