Zimbabwe Politik | Siyasa | DW | 07.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zimbabwe Politik

Hanyoyin fita daga ƙangin rikicin siyasa da yaƙi yaƙi cenyewa a ƙasar Zimbawbe.

default

Mugabe da Tsvangirai sun kasa jituwa


A wannan karo shirin zai je da mu ƙasar Zimbabwe, inda zaumu ji dambarwar siyasar dake wakana, bayan zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, wanda a sakamakon sa shugaba Robert Mugabe yayi tazarce.

Za muji halin da ake ciki da kuma  fadi ka tashin da ake da zumar  warware bakin zaren wannan rikici.


Ranar 27 ga watan Juni na shekara ta 2008 aka shirya zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a ƙasar Zimbabwe, bayan zagayen farko da ya wakana 29 ga watan Maris, inda ƙuri´un shugaban Jam´iyar adawa Morgan Tchangirai suka zarta na Robert Mugabe.

To saidai ta la´akari da matakin da jam´iyar adawa ta MDC ta ɗauka, na ƙauracewa zagaye na biyu , ɗan takara Mugabe shi kaɗai ya shiga  a zaɓen, bayan ƙidayar ƙuri´u, hukumar zaɓe ta tabbatar da cewar ya samu gagaramar nasara.

A game da haka, Robert ɗan shekaru 84 a duniya zai ƙara share wasu shekaru biyar akan karagar mulkin Zimbabwe, bayan shekaru 28 da ya riga yayi ya na jagorancin wannan ƙasa.

Zaɓen na Zimbabwe, ya jawo kace nace a ciki da wajen ƙasar, tsakanin magoya bayan Mugabe da na Tchangirai.

Wannan ƙiƙi ƙaƙa, ta ƙara saka talakawan ƙasar cikin wani mawuyacin hali.

Jama´ar ƙasar baki ɗaya na yi wa kansu tambayoyi a game da ranar da za a samu masalaha, da kuma hanyoyin da za abi domin sasantawa  tsakanin ɓangarorin biyu masu gaba da juna.

Tuni dai ana ta ɓangare Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana matuƙar damuwa a game da halin da Zimbabwe ke ciki,ta kuma yi alƙawarin taimakawa domin fita daga gacci, kamar yadda Sakatare Jannar Ban Ki Mon ya nunar: Wannan halin rikita rikitar siyasa da ake ciki a Zimbabwe na da illoli masu yawa a duk yankin , kuma magance shi na matsayin zakaran gwajjin dafi ga demokraɗiya a Afrika baki ɗaya.

Saboda haka zamu iya ƙoƙarin mu domin samun mafita.

Hausawa kan ce wai a dama dawo ta daɗe ga mai jin yinwa, duk da cewar akwai yunƙuri iri dabam dabam na magance rikicin siyara Zimbabwe, har yanzu babu wanda yayi tasiri.

A taron ƙolin Ƙungiyar Tarayya Afrika a Charm El Cheick shugabanin ƙasashe ko na gwamnatocin Afrika sun shawarci girka gwamnatin haɗin gambiza tsakanin jam´iar Zanu PF da jam´iyun adawa wanda itace hanyar kawo ƙarshen wannan taƙƙadama, to saidai ba da wata wata ba MDC ta yi watsi da wannan shawara, Sakatare Jannar na Jam´iyar Tendai Biti ya bayyana hujjojin ɗaukar wannan mataki: Mu dai a namu ɓangare ba zamu shiga wannan gwamnati ba, ta haɗin gwiwa domin akwai hazo ƙwarai da kuma ayoyin tambaya tattare da wannan shawara,shin gwamnati ce irin ta riƙwan ƙwarya ? sannan shekaru nawa zata yi, koko kawai za ta aiki ne a duk  tsawan shekaru biyar da Mugabe yace an zaɓe shi, shin Mugabe zai girka gwamnati tare da haɗin kan jam´iyun adawa kokuma Morgan Tchangirai zai girka ta, tare da taimakon Zanu PF, gaskiya akwai hazo sosai a cikin al´amarin".

Tendai Biti ya cigaba da cewa, girka gwamnati gambiza ba hanyar da ta fi dacewa ce ba wajen warware rikicin Zimbabwe,abu  mafi a´ala, shine gudanar da kwaskwarima ga kudin tsarin mulkin ƙasar baki ɗaya, da kuma sake saban zaɓe shugaban ƙasa, wanda zai samu halartar ´yan kallo daga ƙasashen ƙetare.

Ƙungiyar Tarayya Turai ta bada haɗin kai ga shawara girka gwamnatin gambiza, amma da sharaɗin MorganTchangirai da ya samu rinjaye a zagayen farko ya zama shugaban gwamnati, matakin da Robert Mugabe yayi watsi da shi ya kuma ci gaba da cewa:Nine shugaban ƙasar Zimbabwe, babu tababa a game da haka,kuma duk mai son tattanawa tare da mu, sai ya amince da wannan sharaɗi.

A yayin da ya maida martani ga kalamomin Robert Mugabe Firaminstan Engla,ƙasar da ta yi wa Zimbabwe mulkin mallaka, ya gayyaci ƙasashen duniya su taru su ceto Zimbabwe ta hanyar ware Mugabe.

Gordon Brown ya kara da cewa:Ina fata Ƙungiyar Tarayya Afrika da Majalisar Ɗinkin Duniya su gama ƙarfi wajen ɗaukar mataki ƙarara akan Robert Mugabe, wato su matsa mashi lalle a sake lale,a kuma tabbatar da cikkakar demokraɗiya a wannan ƙasa idan hakan ta tabbata a shirye muke mu bada taimakon da ya dace ga al´ummomin Zimbabwe.

Wannan ra´ayi na Britaniya ya zo daidai da na kasar Amurika wadda tunni ta gabatar da shwarwari ga komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya a game da hanyoyin warware rikicin siyasar Zimbabwe.

Amurika ta buƙaci komitin Sulhu ya haramtawa shugaba Robert Mugabe tare da wasu muƙarraban sa su 12 fita daga ƙasar Zimbabwe, sannan a sakawa kuɗaɗen da suka mallaka a bankunan ƙetare takunkumi.

A ɗaya wajen Amurika ta shawaraci daina saida makamai ga ƙasar Zimbabwe.

Daga ɓangaren ƙasashen Afrika ma, wasu shugabanin sun bada haɗin kai ga daukar matakin ladabtarwa akan Robet Mugabe.

Alal misali ƙasar Botswana ta bayyana sanarwar inda ƙarara ta yi Allah wadai ga abunda hukumomin Gaborone suka kira murɗiyar da Mugabe yayi domin ya dawwama  akan karagar mulki.

Shi kuwa Firaministan ƙasar Kenya Raila Odinga, ya bayyana buƙatar mayar da Mugabe saniyar ware:A ganina ya kamata Ƙungiyar Tarayya Afrika ta maida Robert Mugabe saniyar ware, har sai lokacin da ya sake shirya zaɓe cikin adalci.

Wasu jama´a da dama na zargin shugaban Afrika ta kudu Tabon Mbeki da Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yankin kudancin Afrika wato SADC ta naɗa a matsayin mai shiga tsakani da nuna fifiko ga ɓangaren Robert Mugabe, a saboda haka mataimakiyar jam´iyar MDC Thokozani Khupe tai wannan kira: Muna kira ga Ƙungiyar Tarayya Afrika ta aika wakili na mussamman wanda zai haɗa ƙarfi da Tabon Mbeki, sannan muna buƙatar aika rundunar shiga tsakani ta ƙasa da ƙasa a Zimbabwe domin a halin da ake ciki, jama´a na cikin haɗari.

A game da halin tsaro a wannan ƙasa, jam´iyar adawa ta MDC ta zargi magoya bayan Zanu PF da jami´an tsaro, da hallaka magoya bayanta fiye da 100, sannan fiye da dubu 10 suka ji raunuka.

kazalika, ƙiddidigar da adawa ta gudanar ta gano cewar, akwai fiye da mutane dubu biyar magoya bayanta, wanda suka yi kasa ko sama.

A taƙaicen taƙaicewa ,rikicin Zimbabwe, babban ƙalubale ne  ga Majalisar Ɗinkin Duniya, da Ƙungiyar Tarayya Afrika, kasancewa har yanzu babu alamun kaiwa ga tundun dafawa, ta la´kari da turjewar da ɓangarorin biyu suka yi.