Zimbabuwe: Mugabe ya sake zama dan takara | Labarai | DW | 17.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Mugabe ya sake zama dan takara

Jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin Zimbabuwe ta sake zaben Shugaba Robert Mugabe a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2018.

Jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar Zimbabuwe a wannan Asabar ta sake tsayar da Shugaba Robert Mugabe dan shekaru 92 da haihuwa a matsayin dan takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2018. Dubban magoya bayan jam'iyyar sun yi ta shewa suna jinjina wa shugaban wanda ya shafe shekaru 36 kan madafun iko, tun da kasar ta samu 'yanci a shekarar 1980 daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Haka na nuna Shugaba Mugabe yana neman tsawaita mulkin da ya yi na tsawon shekaru 36. Yanzu haka kasar ta Zimbabuwe tana fuskantar matsalolin tattalin arziki da hauhawar tashin farashin kayayyaki abin da ya janyo watsi da kudin kasar a shekara ta 2009, inda aka rungumi amfani da kundin kasashen ketare.