1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen fidda gwani na jam'iyar Republican a Amurka

March 7, 2012

Mit Romney ya samu nasara a gaban abokin takara sa Rick santorum a jihar Ohio da yar guntuwar tazara

https://p.dw.com/p/14GCq
Republican presidential candidate and former Massachusetts Governor Mitt Romney speaks at a town hall meeting campaign stop at USAeroteam in Dayton, Ohio March 3, 2012. REUTERS/Brian Snyder (UNITED STATES - Tags: POLITICS ELECTIONS) // eingestellt von se
Hoto: Reuters

A zaɓen fidda gwani na ɗan takarar jam'iyar Republican wanda zai ƙalubalanci Barack obama a zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba da ke tafe.A cikin kashi 99 na ƙuri'un da aka ƙidaya Mit Romney ya samu kashi 38 cikin ɗari ya yin da abokin takara sa Santorum ke da kashi 37.Daman tun can da farko mista Romney ya samu nasara a jihohin Massachussetts wacce ya taba riƙewa a matsayin gwamna ,da Vermont da kuma Virginie ya yin da Rick Santorum ya samu nasara a Tannessee da kuma Oklahoma.

Wannan zaɓe dai ya na cike da mahimanci a fuskar siyasar Amurka wanda masu lura da al'ammura siyasa ke hasashen cewar Mit Romney zai iya taka muhimiyar rawa a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a ƙarshen wannan shekarar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh