1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen cike gurbi na 'yan majalisun dokoki a Nijar

May 15, 2011

Ana sake zaɓen ne dai a jihar Agadez da ke a yankin arewacin Nijar saboda kura kurai da aka samu a zaɓɓuɓukan baya a jihar

https://p.dw.com/p/11GIf
Brigi Rafini Firimiyan NijarHoto: DW

Al'umma na kaɗa ƙuri'a a zaɓen cike gurbi na 'yan majalisun dokokin a jihar Agadez da ke a yankin arewacin ƙasar Nijar. Kujeru shidda ne 'yan takara na jam'iyun siyasa daban daban har guda tara za su nema a zaɓen wanda shine matakin ƙarshe na dadale zaɓuɓɓukan da suka sake mayar da ƙasar bisa tafarki na dimokkaraɗiya bayan zaɓen shugaban ƙasa da na ƙananan hukumomi da aka yi a cikin watannin da suka gabata.

Yanzu haka zaɓen na gudana cikin ƙwanciyar hankali kuma shugaban tawagar masu saka ido Abdu Incirwa ya shaida mana cewa sun aike da wakilai ko'ina a cikin jihar wanda suke yin la'akari da yadda zaɓen ke gudana domin kaucewa aikata maguɗi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman