1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zawarcin wanda zai maye gurbin Jacob Zuma

January 10, 2017

Shekaru biyu gabanin zaben shugaban kasa a Afirka ta Kudu, 'yan siyasa sun fara zawarcin jiga-jigan jam'iyyar kasar mai mulki don karbar ragamar shugabancin kasar da zarar wa'adin Shugaba Jacob Zuma ya kare

https://p.dw.com/p/2VZtW
Dlamini-Zuma und Jacob Zuma
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Prinsloo

Daya daga cikin wadda sunayesu ke mamaye bakunan 'yan jam'iyyar ta ANC mai mulki ita ce Nkosazana Dlamini Zuma, tsohuwar mata Shugaba Zuma. Kiraye-kirayen da ake yi wa Dlamini-Zuma na ta nemi takaran shugabancin Afirka ta Kudu na kara zafafa don a baya-baya nan kungiyar mata ta jam'aiyyar ANC da ke mulki a kasar ta ce, ba za ta mara wa kowa baya wajen samun amincewar uwar jama'iyyar, don yin takara a zaben gama-gari na 2019, face Nkosazana Dlamini-Zuma wadda ke zaman tsohuwar mai dakin shugaban kasar mai ci Jacob Zuma. Kungyiar matan ANC din wadda ke da karfin fada a ji a jam'iyyar, ta ce lokaci ya yi da za a basu dama su fidda wanda zai jagoranci jam'iyyar, kana ya kasance wanda zai mata takara kuma a wannan karon sun yanke hukuncin cewar Dlamini-Zuma ce wadda za su cicciba don ta kai ga wannan matsayi.

Südafrika Zuma hält Rede im Orlando Stadion in Soweto
'Yan jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu sun fara kokarin neman wanda suke so ya zama shugaba bayan karewar wa'adin Jacob ZumaHoto: Reuters/J. Oatway

Wannan batu dai ya sanya maida martani iri-iri da hangen samun rabuwar kawuna a jam'iyyar wadda dama ta fuskanci koma baya a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a bara, kana shugabanta kuma mai rike da madafun iko a kasar Jacob Zuma ke ci-gaba da matsin lamba na ganin ya sauka daga mulki, sakamakon zargin da ake masa da wasu na hannun damansa na yin sama da fadi da dukiyar kasa da kuma yin amfani da matsayinsa ba isa ka'ida. Wannan ne ma ya sanya bangaren matan jam'iyyar neman a basu daman wannan karon su taka irin tasu rawar wajen jagorantar Afirka ta Kudu. Ga dai abinda daya daga cikin jiga-jigan kungiyar mata a jam'iyyar ANC ta ke cewar.

AU Präsidentin Nkosazana Dlamini-Zuma Archiv 16.07.2012
Kungiyar mata ta jam'iyyar ANC a Afirka ta Kudu na son Dlamini Zuma ta zama shugabar kasa ta gabaHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

"Nkossazana Dlamini-Zuma ta jima ta na gwagwarmaya, kuma baya ma ga haka ai ta rike mukamai da dama a jam'iyyar ba wai bangaren mata kadai ba. kazalika ai a nahiyar Afirka ta taka rawar a zo a gani domin ta riki mukamai da dama".

Wadannan batutuwa da aka lissafa dai na zaman misali na irin kwarewar da Dlamini-Zuma ta ke da shi wanda a ganin kungiyar matan jam'iyyar ANC abubuwa ne da za su taimaka mata wajen shugabantar kasar. To sai dai a daura da wannan, a share guda wasu na tunanin bai kyautu a ce Dlamini-Zuma ta jagoranci kasar, kasancewar mataimakin shugaban kasa kana mutum na biyu mafi karfin iko a jam'iyyar ANC wato Cyril Ramaphosa, na da dukannin kwarewar da ta kamata kazalika da shi aka yi gwagwarmaya wajen daidaita lamura a kasar, bayan kawar da mulkin wariyar launin fata. Philipp De Wet dan jarida kana mai sharhi kan lamuran siyasa a kasar, na ganin irin kalubalen da Zuma ke fuskanta ka iya yin tasiri maras kyau ga takarar Mr. Ramaphosa.

Cyril Ramaphosa Südafrika Wahlen
Cyril Ramaphosa na daga cikin wanda kungiyoyi da dama ke son ganin ya maye gurbin Jacob Zuma a matsayin shugaban kasaHoto: DW/A. Lattus

"Cyril, bai da wata mafita dangane da batun zargin cin hanci da ake wa shugabansa Jacob Zuma, duba da matsayin da yake da shi. Kazalika sauran 'yan takara musamman ma dai shugabar majalisar dokokin kasar irin wannan kallo ake mata, don kuwa tana daga cikin na kan gaba wajen kare Zuma a wannan zargi da ake masa. Mutum guda da a iya cewa bai cikin wannan zargi ko kuma bai da tabo na zargin cin hanci da ya danganci Zuma ita ce Nkosazana Dlamini-Zuma".

Yayin da Philipp De Wet ke hangen irin matsalolin da Ramphosa ka iya fuskanta, duba da irin mtsalolilin da shugabansa Zuma ke ciki na cin hanci, a share guda wasu na ganin irin goyon bayan da jam'iyyar ANC ke samu musamman daga wasu kungiyoyi na kwadago da masu hannu da shuni, da wuya a iya cewar zai fuskanci matsala a zaben fidda gwamani na jam'iyyar ko ma zaben shugaba kasa idan lokaci ya yi.