1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar amincewa da tsagaita wuta a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
October 28, 2023

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma'a ya kada kuri'ar amincewa da kudirin neman a tsagaita wuta a Zirin Gaza bisa dalilai na jin kai.

https://p.dw.com/p/4Y8lk
USA UN Abstimmungsergebnisse
Hoto: Bebeto Matthews/AP Photo/picture alliance

Da gagarumin rinjaye kasashe mambobi 121 ne suka amince da neman a tsagaita wuta nan take,kasashe 14 ciki harda Isra'ila da Amurka da wasu na yamma suka ki amincewa da hakan yayin da wasu 44 suka kauracewa kudirin.

Kudirin ya bukaci a mutunta dokoki na yaki wajen baiwa fararen hula kariya, gami da shigar da kayayakin agaji ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

To sai dai ko baya ga wannan kudiri, Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a Gaza, wanda ake samun karuwar asarar fararen hula.

Ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce kawo yanzu sama da mutanedubu 7 ne suka rasa rayukansu tun bayan kaddamar da farmakin ramuwar gayya da Isra'ila ta yi kan kungiyar Hamas.