1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZARTAR DA MAJALISAR TURAI.

Zainab Mohammed.November 18, 2004
https://p.dw.com/p/BveU
Jagoran majalisar zarwar EU,Jose Barroso da Wakilansa.
Jagoran majalisar zarwar EU,Jose Barroso da Wakilansa.Hoto: AP

A yau ne yan majalisar dokokin kungiyar gamayyar turai EU,suka zaratar da amincewarsu da sabbin yan majalisar zartarwan kungiyar da aka dauki makonni uku ana cece kuce akai.

Sabon jagoran hukumar zartarwara jose Manuel Barroso,wanda zai haye kujeran mulki ranar litinin mai zuwa ,nan take yayi alkawarin dukawa tukuru kann aiki,tare da lisafa inganta tattalin arzikin turai ,a matsayin batu dazai fi maida fifiko akai.

Yan majalisar turan 449 suka kada kuriar nuna amincewarsu,ayayinda 149 suka nuna adawa,kana 82 suka ki bayyana,wanda ya kamata da an zartar tun a karshen watan oktoban daya gabata.

Hukumar wadda ta kunshi wakilai 24,akarkashin jagorancin Mr Barroso,wadda da ya kamata ta fara aiki tun ranar 1 ga wannan wata da muke ciki,ayanzu ana saran zata fara aiki a birnin Brussels ranar litinin mai zuwa ,bayan samun amincewa da gwamnatocin turai a gobe jumaa.

An tilastawa Mr Barroso ya janye tawagar farko daya gabatar ne,bayan da yan majalisar dokokin sukayi barazanar hawan kujeran naki ,musamman ma a dangane da wakilin Eu daga kasar Italia Rocco Buttiglione.

Sanannen mai tsattsauran raayi na darikar Katolika ,wanda ya kawo sabani sakamakon furucinsa na cewa yin luwai zunubi ne,ya aminci cikin lokaci na karshe da sauka daga mukaminsa,domin bawa wani dan Italia kuma ministan harkokin waje Franco Frattini , daman maye gurbinsa na babban mai sharia.Ayayinda Hungary da Latvia suma suka gabatar da tasu sabbin wakilai.

Tun da jimawa dai majalisar turan ke laakari da wannan mummunana danganataka na cikin gida da kungiyar ke fama dashi,wanda akoda yaushe yake addaban harkokinta na siyasa.Ana dai bawa sabuwar hukumar zartarwar daman warware wannan rikici dake tsakanin manyan kungiyoyi 3 watau masu raayin rikau,da sassauci da rayuwa.

To sai dai gabannin kada kuriun na yau yan majalisar turan sun bukaci duk wani member na hukumar dayayi murabus daga mukaminsa,idan ya sabawa dokarsu.Mr Barroso dai ya amince dayin haka,koda yake bai dauki alkawrin sakin dukkan komissiona daya sabawa dokokin majalisar ba,ko kuma binciken me yasa ya saba.To sai dai har yanzu akwai ayoyin tambaya da dama,akan ayarin na da Mr Barroso kewa jagoranci,musamman ma akan wakiliyar Holland Neelie Kroes,wadda ke fuskantar zargin rikici ,dangane dangantakar ta na cikayya a baya.Ayayinda yan majalisar sukayi gargadin cewa kuriun nuna amincewarsu baya yana nufin,an basu daman yin abunda suke so bane.Akan hakane aka dakatar da Commissioner Kroes,daga mukaminta har sai an kammala binciken wasu rikice rikice uku datake da hannu acikinsu.