1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zartar da hukuncin kisa a Masar

Zulaiha Abubakar
January 2, 2018

A cewar hukumomin kasar ta an zartas da wani hukuncin kisa akan wasu 'yan ta'adda hudu a yau da aka samu da laifin ta'addanci tun ashekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/2qFSV
Präsident Abdel Fattah Al Sisi vor der UN-Vollversammlung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Altaffer

Kazalika gwamnatin kasar ta sake tsawaita zangon dokar ta bacin da aka fara sawa a lokacin da aka kai wa wasu Coci wani mummunan hari a watan Afrilun bara, dokar da shugaba Abddel Fattah el Sissi ya kafa a halin yanzu za ta cigaba da aiki har na tsawon watanni uku

Ita dai kasar ta Masar ta yi fama da kungiyar ta'addanci ta IS wacce ke da sansani a yankin Sinai, kuma ta ke kai hare-hare a fadin kasar musamman ma ga jami'an tsaro da kuma mabiya addinin Kirista.

Mummunan harin na shekara ta 2015 ya faru ne a wani filin wasa a birnin Kafr-el-Sheikh, a inda wadansu daliban makarantar horas da sojoji suke jiran motar da za ta kai su makaranta.

Zartar da hukuncin kisan da aka yi wa mutane hudun ta hanyar rataya, an yi shi ne a wani gidan yari da ke garin  Alexandria wanda hakan ya kawo adadin wadanda aka samu da laifin ta'addanci kuma aka zartas musu da hukuncin kisa zuwa mutane 19 daga makon daya gabata zuwa yau. Sai dai kungiyoyi da masu rajin kare hakkin 'dan Adam na cewa akwai kura-kurai cikin yadda ake yanke hukuncin .