Zargin wasu Jamusawa da leƙen asiri a Iran | Labarai | DW | 16.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin wasu Jamusawa da leƙen asiri a Iran

Tashar telebijin na gwamnatin Iran ta nunawa duniya Jamusawan da hukumomin ƙasar ke zargi da leƙen asiri

default

Sakineh Mohammad Ashtiani

Ƙasar Iran ta nuna wasu Jamusawa 'yan jarida a gidan talabijin ɗin ta na ƙasa. 'Yan jaridar waɗanda ke tsare na tsawon makonni biyar yanzu, an kama su ne a yayin da suke hira da ɗan wata mata 'yar asalin Iran ɗin wadda aka yanke wa hukuncin kissa ta hanyar jefewa sakamakon samun ta da laifin aikata zina.

Tashar talabijin ɗin ta yi zargin cewa takardun izinin shiga ƙasar da 'yan jaridun biyu ke riƙe da su na yawon buɗe ido ne ba na aikin jarida ba, kuma suna zargin su da ɗaukar hotunan gidan yarin da ke Tabriz, arewa maso yammacin Iran inda ake tsare da matar.

Wannan lamari na Sakineh Mohammed-Ashtiani ya tayar da muhawara a tsakanin al'ummomin ƙasa da ƙasa a 'yan watannin da suka gabata bayan da ƙungiyoyin da ke kare haƙƙin bil adama suka bayyana batun. Haka nan kuma, wata ƙungiyar 'yan jarida a Jamus ta ce zargin da ake wa 'yan jariduu da yin leƙen asirin ba shi da hujja.

A halin da ake ciki yanzu, ƙasar Faransa ta nuna adawar ta da ƙasar Iran bayan da ta tsare waɗansu manyan baƙin ta da suka ziyarci ofishin jakadancin Faransar da ke Tehran a ranar Lahadin da ta gabata. Wani jami'i a ofishin kula da harkokin wajen Faransa ya ce mutane kimanin 30 kaɗai daga cikin baƙi 130 da suka ziyarci wurin suka iya shiga a yayin da aka tafi da waɗansu a cikin manyan motoci.

Ƙasashen Faransa da Iran suna fama da rashin jituwa a 'yan kwanakin nan tun bayan da Faransa ta goyi bayan takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya wa Iran bisa shirin ta na makamashin nukiliya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammed Abubakar