Zargin tafka maguɗi a zaɓen Gini | Labarai | DW | 29.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin tafka maguɗi a zaɓen Gini

Wasu jam'iyyun da suka shiga zaɓukan Gini sun yi zargin tafka almundahana saɓanin abinda masu sa ido suka faɗi

default

Babbar darektar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugabancin ƙasar Gini a ƙarƙashin tutar jam'iyyar PEDN Zalikhatu Diallo ta yi zargin cewar, an tafka maguɗi a manyan biranen ƙasar guda biyu a lokacin babban zaɓen da ƙasar da ta gudanar - ranar Lahadin da ta gabata. Ta ce, akwai akwatunan da aka sace a daren zaɓen, a biranen Conakry da Sigiri, waɗanda kuma aka mayar da su da safe bayan aringozon ƙuri'u a cikin su.

Zalikhatu Diallo, wadda ke goyon bayan Lansana Kuyate dake neman shugabancin ƙasar, ta ce tuni jam'iyyar ta gabatar da wannan koken ga hukumar zaɓen ƙasar - mai zaman kanta wato CENI. Kuyate, wanda shekarun sa na haihuwa 60 ne a duniya, ya taɓa riƙe muƙamin Firaministan Guinea tsakanin watan Maris na 2007 zuwa Mayun 2008 a ƙarƙashin shugabancin marigayi Lansana Konte, wanda ya mutu a shekara ta 2008 bayan da ya mulki ƙasar na tsawon shekaru 24.

Hakanan kuma jam'iyyar wani tsohon Firaministan ƙasar Salihu Diallo da shima ke neman shugabancin ƙasar, ita ma ta yi zargin cewar an tafka maguɗi a zaɓen - duk kuwa da cewar masu sanya ido suka ce zaɓen ne mafi nagarta tun bayan da ƙasar ta samu nyanci daga Faransa a shekara ta 1958. Jam'iyyar sa ta UFDG ta kuma yi zargin cewar hukumar zaɓen na yin jinkiri wajen fitar da sakamakon zaɓen.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijjani Lawal