Zargin ta′addanci a Jamus | Labarai | DW | 05.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin ta'addanci a Jamus

Masu shigar da ƙara a Jamus sun zargi wasu mutane da tallafawa ayyukan ta'addanci

default

Masu gabatar da ƙara a birnin Stuttgart da ke nan Jamus sun gurfanar da wasu mutane ukku a gaban wata kotu, bisa zargin suna bayar da horo ga matasa musulmi domin aikata ta'addanci. Wani kakakin masu shigar da ƙara ya ce ana zargin mutanen da hannu wajen ɗaukar nauyin biyan kuɗaɗen karatu ga matasa Jamusawan da suka musulunta, domin halartar karatun al-Qur'ani - mai tsarki a ƙasar Masar, inda ake zargin daga nan kuma sai a haɗa su da waɗanda ke koya musu tsattsauran ra'ayin ta da tarzoma. Ana dai zargin matasa da dama ne suka halarci sansanonin bayar da irin wannan horon.

Idan za'a iya tunawa dai a watannin baya wata kotu a birnin Duesseldorf da ke nan Jamus ta yankewa wasu mutane huɗu hukuncin zaman gida yari bisa samun su da laifin yunƙurin ƙaddamar da hari makamancin na 11 ga watan Satunmbar 2001 a ƙasar Amirka.

Harin wanda suka nufi kaiwa sojin Amirka da kuma fararen hula a Jamus bai yi nasara ba. Daga cikin waɗanda kotun ta yankewa hukuncin harda Jamusawa biyu da suka musulunta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammad Nasir Awal